HAUSA: Rahoton Dake Yawo A Yanar Gizo Dake Cewa Okonjo-Iweala Ta Zama Shugabar WTO KARYA NE

Share

Fassara da Mai rawaitowa: Musa Sunusi Ahmad.

Marubuci: Olugbenga Adanikin.

 

A ranar Laraba, 28 ga watan Goma, 2020, kafafen yad’a labarai da dama a Najeriya ne suka rawaito cewa Ngozi Okonjo-Iweala ta zama shugabar Kungiyar Cinikayya Ta Duniya WTO.

Okonjo-Iweala tsohuwar ministan kudi ce, haka kuma tsohuwar ministan gudanarwa ce ta tattalin arzikin Najeriya.

Ita da Yoo Myung-Hee ta kasar Koriya ta kudu ne suka rage dake fafatawa wurin neman kujerar shugabancin WTO.

 

IKIRARI

Ngozi Okonjo-Iweala ta zama shugabar Kungiyar Cinikayya Ta Duniya WTO

 

BINCIKE

A binciken da FactCheckHub yayi ya nuna rahoton KARYA NE.

Vanguard Newspaper dake da miliyoyin mabiya ta rawaito labarin cewa Okonjo-Iweala ta zama shugabar WTO.

Wata sabuwar kafar labarai ta People Gazette itama ta wallafa makamancin labari akan Okonjo-Iweala ta dare kujerar shugabancin WTO.

Cikin kankanin lokaci rahoton ya samu mutane 2,600 da suka nuna sonsu da rahoton, inda kimanin mutane 1,800 suka yad’a labarin dake a fejin @GazetteNGR na Twitter. Inda aka fara koka labarin tare da tura sakon taya murna.

People Gazette ta ayyana tare da yin togaciya a rahoton ta, da labarin da Gidan talabijin na Arise Television yayi tun farko da misalin karfe 12:30 na yamma na ranar Laraba (28 ga watan Goma).

Newswire ma tabi sahu, amma ta sabunta labarin ta daga baya, bacin da aka fara kalubalantar kafafen yad’a labarai kan dalilin da yasa suka zabi cewa suyi rahoton batare da jiran WTO ta sanar a hukumance ba.

Har izuwa yanzu da muke tattara binciken mu, ba wani bayani a hukumance dake cewa Okonjo-Iweala ta zama shugabar WTO koda a fejukan WTO na sada zumunta.

 

LABARIN IZUWA YANZU….

A ranar 28 ga watan Goma, gun mambobin WTO sun bada shawarar nada Okonjo-Iweala matsayin wadda zata jagorancin WTO, amma kasar Amurka tayi watsi da haka.

Kafar yad’a labarai ta Bloomberg ta rawaito cewa inba dan matsayar kasar Amurka ba, da tuni WTO ta gabatar da tsohuwar ministan kudi ta Najeriya amatsayin sabuwar shugabarta.

Duk da cewa Okonjo-Iweala ruwa biyu ce, Najeriya-Amurka, amma kasar Amurka ta ayyana yar takarar Koriya ta kudu Yoo Myung-Hee amatsayin zabinta. Gwamnatin Amurka ta koka kan cewa fadar Washington ba zata dau yar Najeriya ba, amatsayin wadda zata jagorancin WTO ba. Duk da shawarar babban zauren bai daya na Kungiyar kan Okonjo-Iweala.

Har izuwa yanzu da muke tattara binciken mu ba wata sanarwa a hukumance dake ayyana Okonjo-Iweala matsayin sabuwar shugabar WTO. Kuma babu wani bayani hakan akan fejin su na twitter@wto ko fejin su na yanar gizo.

Saboda matsayar Amurka, zauren bai daya dake da alhakin gudanar da zaben ya daga sanar da sabuwar shugabar har sai 9 ga watan Sha Daya na 2020.

Wannan ba shine karan farko da labarai marasa tushe akan takarar neman kujerar shugabancin WTO ke kara-kaina a fejukan yanar gizo ba. FactCheckHub ya bankado irin wannan labarai a lokuta mabambanta a watan bakwai nan da watan Goma nan wanda duka basu da tushe.

 

HUKUNCI

Duba da irin bayanai dake akwai, babu wani bayani a hukumance da zai tabbatar da ikirarin cewa Ngozi Okonjo-Iweala ta zama shugabar WTO. Dan haka labarin KARYA NE.

Kawai dai zauren bai daya na WTO ya bada zabinta.

 

Samunta:

A watan Fabrairu 2021 ne aka tabbatar da Okonjo-Iweala a matsayin Shugabar Kungiyar Cinikayya Ta Duniya WTO

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here


Most Read

Recent Checks