HAUSA: Rubutun Dake Yawo Cewa Gwamnatin Tarayya Tana Temakawa Yan Najeriya Da Tallafi Ba Gaskiya Bane

Share

Fassara da Mai rawaitowa: Musa Sunusi Ahmad.

Marubuci: Samad Uthman.

 

Wani rubutu dake yaduwa a dandalin zumunta na Whatsapp wanda ke cewa Gwamnatin Tarayya tana bada tallafi dan dan temakawa yan Najeriya.

Rubutun ya cigaba da fadin cewa tallafin na miliyan uku ne kuma gurbin mutane 9,540 kawai, kuma za’a bada tallafin ga wayanda suka fara shiga tsarin.

 

IKIRARI:

Gwamnatin Tarayya Ta Najeriya Ta fara bada tallafin miliyan uku-uku dan temakawa yan Najeriya.

 

ABUN DA MUKA GANO:

Binciken mu ya gano cewa labarin karya ne.

Duk da cewa rubutun bai tabbatar da irin yadda tallafin yake ba, amma cibiyar ICIR ta ziyarci fejin yanar gizo dake yada likau din shiga tsarin dan tabbatar da gaskiyar labarin.

Wakilin mu da ya bibiyi likau din shiga tsarin mai suna “bonanzaoffers.xyz”. Bacin shigarsa fejin sai wani allo ya bayyana yana dauke da cewa ” Muna taya ka murna da shigowa wannan feji kuma muna ma albishir zaka iya samun tallafin biliyan 75 daga Gwamnatin Tarayya”, zuke fadawa wakilin mu.

Aka cigaba da yi masa tambayoyi akan dalilin da yasa yake so ya shiga tsarin; da kuma adadin da mutun yake so ya nema, tare da neman sanin ta yaya kasan tsarin. Kuma duka tambayoyin suna dauke da zabi daban-daban.

Cikin dakiku hudu da danna “Turawa”. Kawai sai aka aikowa wakilin ICIR cewa ya samu nasarar shiga jerin wayanda suka samu nasarar samun tallafin.

Amma dan sakin kudun sai akace dashi sai ya turawa abokansa ko kuma zaurukan Whatsapp guda goma Sha Biyu. A cewar fejin yanar gizon, yin haka zai bawa sauran yan Najeriya su ci moriyar tsarin.

Duk da haka, sai ICIR ta gudanar da wani bincike ta amfan da fejin kowace tambaya wato”Google” inda tai tambaya kamar haka, dan gano gaskiyar tsarin bada tallafin na Gwamnatin Tarayya; ” tallafin biliyan 75 na Gwamnatin Tarayya”.

Saidai amsar ta nuna tsarin tallafin farfado da Kanana da Matsakaitan Sana’oi wato (MSMEs) wanda ake kira da ” MSME Survival Fund.

Tsarin an samoshi ne daga kwamitin daurewar tattalin arziki wanda aka yishi dan tsara yadda za’a magace irin kalubalen da annobar cutar sarkewar numfashi ta coronavirus pandemic ta kawo na tabar-barewar tattalin arziki.

Tsarin da aka tsara za’a gudanar dashi tsawon wata uku, farawa da watan Tara na 2020, wanda Ma,aikatar Kasuwanci, Ciniki Da Zuba Jari Ta Tarayya zata kula dashi. Inda ake sa ran yan kasa da kamfanunuwa miliyan 1.7, wanda kaso 45 na wayanda za suci gajiyar tsarin matane masu Sana’oi, kaso biyar 5 kuma masu bukata ta musamman.

Wani tsarin biliyan 75 na Gwamnatin Tarayya da ICIR ta gano yayin binciken ta, shine Asusun Zuba Jari Na Matasa wato “Nigerian Youth Investment Fund (NYIF) wanda yake karkashin kulawar Maaikatar Matasa Da Cigaban Wasani Ta Tarayya. Tsarin da babban bankin Najeriya wato CBN sai dinga tallafa da kudaden gudanarshi, zai dauki tsawon shekara uku yana tallafar Kasuwanci matasa a Najeriya.

Tsarin na bashi ne, wanda ke dauke da kaso 5 na kudin ruwa a shekara da kuma za’a biya cikin shekara biyar dake dauke da uzurin watanni Sha Biyu. Inda dai daikun mutane da kasuwaci mara rijista zai iya karbar kudi har kimanin dubu 250’000, inda kuma kamfanunuwan matasa masu rijista zasu iya karbar kudi har miliyan uku.

Wannan shine hanyoyin da kirkirarran fejin yanar gizon yake bi yayin tambayar daidaikun mutanen suke so su karba daga dubu #200’000 har miliyan uku.

 

Su waye yan damfarar?

Cibiyar ICIR tabi diddigin fejin yanar gizon na karya dan samo bayanan mamallakansa ta hanyar amfani da manhajar yanar gizo ta Whois.net.

Har izuwa yanzu da muke hada wannan rahoto, ba wani bayani na fejin, kamar yadda aka saba gani a sauran fejikan yanar gizo.

Duk da cewa binciken mu be gano ko a ina kuma su waye suka kirkiri fejin yanar gizon ba. Amma mun gano an kirkiri fejin yanar gizon ranar 08/05/2020 kuma an debar masa tsawon shekara guda yana gudana.

Sauran bayanai da suka hadarwa nambar waya da akwatin karta kwana na yanar gizo wato “email” duka babu su.

 

HUKUNCI:

Labarin KARYA NE, kuma fejin yanar gizon ba wai kawai kirkirarre bane, amma samar dashi dan yada labarai marasa tushe.

Website | + posts

Opeyemi Kehinde is a Professional Fact-Checker, Multimedia Journalist, and Editor of the FactCheckHub.

1 COMMENT

  1. Mu aduarmu shine Allah yabamu zaman lafiya a Nigeria Kuma yasa wanna shugaban kasan ya kasance adali Kuma Mai tausayi Mai cika alkauwari Sanna duk yanda shugaba yakasance baha zaginsa yanhuwana Yan Nigeria adu,a akeyi she Allah yakawo sauki

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here


Most Read

Recent Checks