Fassara da Mai rawaitowa:Â Musa Sunusi Ahmad.
Marubuci: Niyi Oyedeji.
A ranar Litini 2 ga watan Sha Daya, 2020, fejin yanar gizo na kaida halinka da dama ne a Najeriya suka rawaito cewa shugaban Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO, Tedros Ghebreyesus ya kamu da cutar sarkewar numfashi ta COVID-19.
Wasu daga cikin fejikan da suka wallafa rahoton sun hadarwa Sahelstandard, Bioreports, Naijanews, Business247news da kuma Sunrise.
Kafofin yad’a labaran sun ce shugaban Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO da kanshi ya sanar da halin da yake kan cutar a fejin sa na Twitter.
“An auna shugaban Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO Tedros Ghebreyesus, kuma awon ya nuna ya kamu da cutar sarkewar numfashi ta coronavirus”.
Inda rahoton Naijanews yake cewa; “Shugaban Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO ya sanar da halin da yake ciki a cikin jerin takaitattun gajerun wallafe-wallafe da yayi akan tabbataccen fejin na Twitter”
IKIRARI:
Wai shugaban Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO Ya Kamu Da Cutar Sarkewar Numfashi Ta COVID-19.
ABINDA MUKA GANO:
FactCheckHub ta duba gajerun takaitattun wallafe-wallafe da shugaban Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO yayi, musamman wanda masu fejinkan kaida halinka suka dogara dashi wajen rubuta rahoton su.
A ranar 1 ga watan Sha Daya,2020. Shugaban WHO, Tedros Ghebreyesus ya rubuta a Twitter cewa; an gano nayi alaka da wani da aka gano ya kamu da cutar sarkewar numfashi ta COVID-19.
Ghebreyesus bai rubata an aunashi yana da cutar sarkewar numfashi ta COVID-19 acikin rubutunsa na Twitter ba.
Yadai kawai ce zai killace kansa a yan kwanakin nan gani halin da ake ciki.
Haka kuma, a washe garin ranar 2 ga watan Sha Daya, 2020. Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO ta bayyana gaskiyar halin da ake ciki akan cece kucen dake yawo kan shugaban hukumar na halin dake ciki akan cutar sarkewar numfashi ta COVID-19.
WHO ta tabbatar da cewa Ghebreyesus bai kamu da cutar sarkewar numfashi ta COVID-19 ba.
FactCheckHub ya rawaito cewa mambobin WHO sun zabi dan kasar Habasha, Dr Tedros Ghebreyesus yayin taron Zauren Lafiya Na Duniya, karo na bakwai, a watan biyar na shekarar 2017.
HUKUNCI:
KARYA NE cewar shugaban Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO, Tedros Ghebreyesus ya kamu da cutar sarkewar numfashi ta COVID-19; kawai dai yayi alaka da mutumin da wani mutum da aka gano yana da cutar.
Opeyemi Kehinde is a Professional Fact-Checker, Multimedia Journalist, and Editor of the FactCheckHub.