[thim-heading title=”Hausa Fact-Check Videos” title_uppercase=”” clone_title=”” line=”true”]
Videos in compliance with YouTube’s Terms of Use and Privacy Policy

ManCity iƙirarin karya akan dan wasa daya da ya saka bajon zakarun duniya na kungiya da kasa

Kungiyar Manchester City tayi iƙirarin karya akan dan wasa daya da ya saka bajon zakarun duniya na kungiya da kasa

Manchester City tayi iƙirarin ɗan wasan gabanta Julian Alvarez ne kaɗai ...
ya taɓa saka bajon zakarun duniya na kungiya da kuma na ƙasa a duniya.

Ƙungiyar tayi wannan iƙirarin ne a X ranar 28 ga watan Disambar 2023 yayin murnar nasarar da tayi akan kungiyar Fluminense ta Barazil, a gasar kofin duniya na kungiyoyi da hukumar FIFA ta shirya a ƙasar Saudi Arabia.

Alvarez ya zira ƙwallaye biyu a yayin da ƙungiyarsa ta lashe kofin zakarun na FIFA a karon farko bayan da ta lallasa Fluminense 4-0 ranar Juma’a 22 ga watan Disamba 2023, kamar yadda BBC ta ruwaito.

Wannan ne kofi na biyar da ƙungiyar ta lashe a 2023 bayan Gasar Firimiya, Kofin FA, zakarun turai na UEFA da kuma kofin zakaran zakarun turai.

Hukunci: KARYA NE

Ana bada bajon zakarun hukumar kwallon ƙafa ta duniya ne yayin wani muhimmin biki na FIFA. Kasa ta farko data samu wannan bajo ita ce tawagar kasar italiya ta maza lokacin da suka lashe gasar ƙwallon kafa ta duniya a 2006.

Kungiyar kwallon kafa ta farko da ta fara samun wannan bajon itace AC Milan bayan ta lashe kofin zakarun duniya na kungiyoyi da FIFA ta shirya a 2007.

Bincike ya nuna kafin Alvarez, ɗan wasan baya na Manchester United, Raphael Varane ne ya kai wannan matsayi bayan ya taimakawa Faransa ta lashe kofin duniya a karo na biyu da kuma Real Madrid ta lashe kofin zakarun turai na 13 da kofin zakarun duniya na kungiyoyi da FIFA ta shirya a 2018.

Wannan ya nuna Varane ya riga Julian Alvarez samun wannan bajon a rigarsa ta kungiya da kuma ta ƙasa.

END CREDITS:
Rubutawa: Nurudeen Akewushola
Fassara: Ali Isa Musa
Mai ba da Labari: Musa Sunusi Ahmad

Kara koyo: https://factcheckhub.com/man-city-makes-false-claim-about-only-player-to-wear-world-champion-badge-for-club-country/
[+] Show More
1 of 6